3 Nuwamba 2016 - 11:10
A Cikin Sakonsa Na Farko Dangane Da Yakin Musil Shugaban ISIS Yace Nasara Tasu Ce

Shugaban kungiyar Daesh Abubakara Bagdadi ya bada wani sakon sauti a karon farko tun bayan fara yakin kwace birnin Musil na lardin Ninawa a kasar Iraqi makonni kimani ukku da suka gabata.

Bagdadi wanda asalin sunansa shi ne Ibrahim al-Samirrai ya bukaci mayakan Daesh wadanda suka ja daga da sojojin kasar Iraqi da masu tallafa masu kan cewa su daga da jihadi don nasara tana gabansu.

Duk da cewa har yanzun ba'a tantance ingancin sautinsa ba amma Bagdadi  ya yi kira ga mayakansa da su kwararar da jinin wadanda ya kira kafirai a cikin kasar Iraqi su kuma maida dararensu rana.

A ranar 17 ga watan Octoban da ya gabata ne Rundunar sojojin kasar Iraqi tare da mayakan sa kai na Hashdushaabi da kuma na wasu kasashen waje suka fara farmakin kwatar tungar mayakan Daesh na karshe a kasar Iraqi, wato birnin Musil. 

Yawan mutane a birnin dai sun kai miliyon 1.5 kuma tun shekara ta 2014 Daes take mamaye da birnin a matsayin cibiyar ta na abinda ta kira daular musulunci.288